Babban mai baiwa shugaban ƙasa shawara a kan al’amuran tsaro a Najefiya Nuhu Ribadu na yin wata ganawa da manyan hafsoshin tsaro da gwamnonin arewa a Abuja.

Duk da cewar ba a bayyana dalilin ganawar ta sirri ba, amma ba ya rasa nasaba da batun sace ɗlibai da aka yi a Kaduna da sauran sha’anin tsaron ƙasar.
Ganawar da aka fara a yau da rana na zuwa ne bayan da ahugaba Bola Ahmwd Tinubu ya bayar da umarnin gaggawa don kuɓutar da ɗaliban.

Gwamnonin Kaduna, Katsina, Zamfara Borno, Nassarawa na daga cikin waɗanda su ka halarci taron.

An yi garkuwa da ɗalibaan firamare sama da 200 a Kaduna yayin da aka sace ɗaliban tsangaya a Sokoto sai kuma ƴan gudun hijira da aka sace a jihar Borno.
Zuwa yanzu ba a bayyana matsaya da kuma abinda aka tattauna a dangane da zaman sirrin da aka yi ba.
