Babban kwamandan hukumar tsaron farar hula a Najeriya NSCDC Ahmed Abubakar Audi ya tabbatarwa da al’ummar jihar Kaduna cewar za su yi duk mai yuwuwa don kuɓutar da ɗaliban da aka sace.

 

Kwamandan ya tabbatar da hakan ne yayin da ya ziyarci gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani kamar yadda mai magana da yawun hukumar Babawale Afolabi ya sanar a yau Alhamis.

 

Kwamandan ya ce ɗalibai sama da 200 da aka sace a Kuriga za su tabbatar sun kuɓutar da su cikin koshin lafiya.

 

Sannan au na haɗa kai da sauran jami’an tsaro don ganin sun ceto ɗaliban.

 

Haka kuma a shirye su ke don aiki da jami’an soji da ƴan sanda da sauran jami’an tsaro don ganin sun tabbatar da kuɓutar da ɗaliban.

 

Gwamna Uba Sani ya yabawa jami’an a kan hadin gwiwar da su ka yi domin ceto daliban.

 

Sannan sun bukaci kungiyoyi su baiwa jami’an tsaron hadin kai don ganin an sami nasara a kai.

 

Sace ɗaliban na daga cikin abubuwan da su ka ja hankalin gwamnati musamman a wannan lokaci da ake ci gaba da samun matsalar tsaro a Najeriya.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: