Helkwatar tsaro a Najeriya ta ce masu garkuwa da ke sace mutane a jihar Borno da Kaduna matsorata ne.

Mai magana da yawun helkwatar Edward Buba ne ya bayyana haka a taron manema labarai da aka gudanar yau a Abuja.


Ya ce masu satar mutanen na amfani da damarsu bayan mutane sun shiga daji ko fakar ido kafin sace mutane.
Ya ce ƴan bindiga na sane da sabbin kayan aiki da jiragen yaƙin da su ke da su, wanda hakan ya sa sai sun faki ido kafin su aikata wani abu.
Buba ya ƙara da cewa masu garkuwa na amfani da satar ɗalubai da mutanen gari dob gudun yi musu ɓarin wuta a maɓoyarsu.
A cewar daraktan, sun samu damar kashe da yawa daga cikin manyan shugabannin ƴan bindigan, wanda hakan ke sanyawa a su nemi mafaka ta hanyar sataryu ɗalibai.
Dangane da ɗalibai da mutanen da aka yi garkuwa da su, darakta Buba ya ce ba za su sarara ba har sai sun kuɓutar da su.
Ko a jiya sai da shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewar za a kuɓutar da ɗaliban da aka sace a Kasuna ba tare da biyan ko sisi ba.
