Hukumar ƙididdiga a Najeriya ta ce an samu hauhawar farashin kayan masarufi a ƙasar da kashi %31.70 cikin watan Fabrairu da ya gabata.

Hukumar ta fitar da ƙididdigar ne bayan da ta tattara alƙaluma dangane da hauhawar farashi da aka samu.


A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce an samu ƙarin hauhawar farashi da kashi 1.80 la’akari da kashi 29.90 na tashin farashi da aka samu a watan Janairu.
A rahoton da ta fitar a yau Juma’a, ta ce hauhawar farashin ya shafi kayan abinci, farashin ruwa da na lantarki, da sauran kayan amfani.
Sannan hauhawar farashin ta shafi kayan lambu da sauran kayan masarufi da ake amfani da su na yau da kullum.
Dangane da farashin man fetur kuwa, hukumar ta ce tashin farashinsa na jingina ne kai tsaye da cire tallafin man fetur.
Idan ba a manta ba, faɗuwar darajar naira ta sake haifar da tsada wanda har ta kai dalar guda amuruka ta kai darajar naira 1,900 a kasuwar bayan fage.
