Babban hafsan sojin ƙasan Najeriya Janar Christopher Musa ya buƙaci hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin kasa zagon ƙasa EFCC ta zaƙulo masu ɗaukar nauyin ƴan bindiga.

Shugaban ya bayyana haka ne yau a Abuja, yayin da ya karɓi baƙoncin shugaban hukumar ta ƙasa Ola Olukoyede.

Ahugaban sojin ya ce zaƙulo masu ɗaukar nauyin ƴan bindigan shi ne babban yaƙin da za su taimakesu da shi kuma ita ce hanyar da za su taimakawa duniya kan sha’anin tsaro.

Bayan da ya tayashi murna a matsayin sabon shugaban EFCC, ya sake jaddada masa cewar, jami’an soji a ƙasar ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an tsame ƙasar daga halin rashin tsaro da ta ke ciki.

Sannan ya sake jaddada cewar, jami’an soji na aiki afaɗa da kafaɗa da kamfanin mai na ƙasa NNPC don magance satar ɗamyen mai a ƙasar.

Da yake mayar da jawabi, shugaban hukumar EFCC Ola Olukoyede ya ce wajibi ne su sake zage damtse don yaƙi da rashawa a Najeriya wanda su ka mayar da hankali a kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: