Jami’an sojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu ‘yan bindiga biyu a wasu hare-haren da su ka kai maboyarsu da ke Jihohin Zamfara, Filato da kuma Imo.

 

Jami’an sun kuma kubutar da wasu mutane hudu da maharan su ka yi garkuwa da su.

 

Mai magana da yawun rundunar Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

 

Onyema ya ce daga cikin wadanda jami’an suka kubutar, sun kubtar da wata mace a kauyen Rafin Buna da ke cikin karamar hukumar Bassa ta Jihar, bayan sun yi musayar wuta da Maharan.

 

Manjo Onyema ya kara da cewa matar da aka ceto maharan sun yi garkuwa da ita ne a gidanta da ke Abuja Layout a karamar hukumar Jos ta Kudu a Jihar ta Filato.

 

Kazalika Nwachukwu ya bayyana cewa jami’an sun kuma kwato bindiga kirar AK47 guda daya babura guda biyu daga hannusu.

 

Har ila yau kakakin ya ce bayan wani kiran gaggawa da jami’ansu suka samu daga Jihar Zamfara, sun dakile wani yunkurin batagarin na yin garkuwa da wasu mutane uku a garin Kwatarkwashi cikin karamar hukumar Gusau a Jihar.

 

Kakakin ya kara da cewa bayan musayar wutar da suka yi da maharan hakan ya sanya suka tsere suka bar mutane.

 

Sannan jami’an sun kuma sake kai sumame maboyar ‘yan ta’addan a Imo inda suka koresu daga maboyar tasu da ke Jihar.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: