Wata kotu da ke birnin tarayya Abuja ta yankewa wani lebura mai suna Terkaa Akishi daurin watanni 15 a gidan ajiya da gyaran hali na birnin.

Kotun ta yankewa leburan mai shekaru 36 hukuncin ne bisa laifin kamashi da satar Alkur’anai da wayar hannu a masallacin Asokoro da ke birnin.


Alkalin kotun mai shari’a Malam Aliyu Kagarko ne ya yankewa mutumin hukuncin a yayin zaman da kotun ta gudanar a ranar Talata bayan amsa laifinsa.
Alkalin ya kuma bashi zabin biyan tarar naira 40,000.
A yayin shigar da kara dan sanda mai gabatar da kara ya bayyana cewa an kai karar wanda ake zargi ne tun a ranar 14 ga watan Maris.
Dan sandan ya ce laifin da wanda ake zargi ya aikata ya ci karo da sashi na 348 da 287 na kundin laifuka.