Biyo bayan taɓarɓarewar matsalar tsaro a Najeriya, gwamnoni 16 sun goyi bayan ƙirƙiro ƴan sandan jihohi.

 

Majalisar tattalin arziƙi ta ƙasa (NEC) ce ta bayyana haka a rahoton da ta miƙa wa majalisar a wurin taron karo na 140 wanda ya gudana ranar Alhamis a Abuja.

 

Taron wanda ya gudana ta hanyar amfanin da fasahar zamani ya kasance ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.

 

Ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren kasa, Alhaji Atiku Bagudu, wanda ya zanta da ƴan jarida ta intanet bayan kammala taron, ya ce sauran jihohin ba su faɗi matsayarsu ba.

 

Bagudu ya bayyana cewa jihohi 20 da babban birnin tarayya Abuja ba su sanar da matsayarsu kan batun kafa ƴan sandan jihohin ba har kawo yanzu.

.

Sai dai Bagudu, tsohon gwamnan jihar Kebbi bai ambaci sunayen jihohin da suka goyi baya da waɗanda suka yi shiru kan lamarin ba.

 

Ya ƙara da cewa gwamnonin da suka mika takardar goyon bayan kirkiro ƴan sandan, sun kuma nemi a sake garambawul ga kundin tsarin mulkin ƙasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: