Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin cewa makasan sojoji Najeriya a jihar Delta ba za su ci bulus su tafi haka kawai ba tare da an hukunta su ba.

Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci hare-haren da ake kai wa dakarun sojoji da sauran jami’an tsaro ba.


Shugaban ya faɗi haka ne yayin da ya karɓi bakuncin shugabannin majalisar dattawa a wurin buɗa bakin azumin Ramadan a fadar shugaban kasa ranar Alhamis.
Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya karƙashin jagorancinsa za ta ci gaba da bai wa sojoji dukkan goyon bayan da suke buƙata domin murƙushe kowane irin ƙalubalen tsaro.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajure Ngelale ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 21 ga watan Maris, 2024.
A sanarwar da babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin hulɗa da jama’a, Fedrick Nwabufo, ya wallafa a manhajar X, Tinubu ya gode wa majalisar dattawa bisa haɗin kan da suka ba shi a mulkinsa.