Hukumar Kula da Tituna ta Kasa FERMA ta koka kan yadda wasu ‘yan kwangila da ba su cancanta ba ke samun kwangiloli na miliyoyin Naira a Jihar Kano.

Muƙaddashin Injiniyan da ke kula da tituna na Tarayya a jihar, Ali Abdu ne ya koka kan lamarin yayin da ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Hukumar FERMA a ranar Talata.


Ali Abdu ya yi wa ‘yan majalisar bayanin kwangilolin da FERMA ta aiwatar a shekarar 2023.
Ya ce, abin takaici, wasu ’yan kwangilar ba su da ƙwarewa, ballantana kayan aiki amma suna samun kwangilar miliyoyin da za su aiwatar.
Ya ƙara da cewa wani ɓangare na matsalolin da hukumar ke fuskanta shi ne rashin ababen hawa na masu aiki saboda waɗanda ake aikin fita sa ido da su ba sa aiki ko kuma suna buƙatar a canza su.
Injiniyan ya ƙara da cewa, titin gwamnatin tarayya da ke kan iyakokin Kano ya kai kilomita 990, yayin da akwai mai tsayin kilomita 423 ke da kyau, sai kuma mai tsayin kilomita 502 da ke da inganci matsaikaci, 502 da kuma mai tsayin, kilomita 32 da ke cikin mummunan yanayi.
Kazalika, ya ce daga cikin kwangiloli guda 16 da aka ware a Kasafin Kuɗin shekarar 2023, an kammala shida kuma ana ci gaba da aikin biyar.
Sai dai ya ce zuwa yanzu sun samu rahoton aikin wani dan kwangila ɗaya amma akwai ‘yan kwangila huɗu da ba su kai nasu rahoton ba.