Hedkwatar tsaro ta kasa ta fitar da sunaye da hotunan mutane 97 da ta ke nema ruwa a jallo bisa zarginsu da aikata ta’addanci a Kasar.

Mai magana da yawun hedkwatar Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
Buba ya ce daga cikin wadanda rundunar ta ke nema ciki harda shugaban kungiyar fafutukar kafa kasar Biafara ta IPOB tsagin Simon Ekpa, tare da karin 96 da ta ke nema.

Hedkwatar ta ce daga cikin wadanda ta ke nema ciki harda ‘yan tada kayan baya, ‘yan ta’adda da sauran masu aikata miyagun laifuka da gurbacewar tsaro a Kasar.

Buba ya kara da cewa su na neman ‘yan ta’addan da suka addabi yankunan Arewa maso gabas, da Arewa maso yamma, sai ‘yan tada kayar baya daga Kudu maso gabas da kuma Arewa ta Tsakiya.
Har ila yau Manjo Buba ya ce hedkwatar na neman ‘yan ta’adda 43 da suka addabi yankin Arewa maso yamma da ke fama hare-haren ‘yan bindiga.
Wasu daga cikin mutanan sun hada da Ado Aliero, Alhaji Shingi, Malindi Yakub, Boka, Dogo Gide, Halilu Sububu, Bello Turji, Dan Bokkolo, Labi Yadi, Nagala, Sa’idu Idris, Kachalla Rugga da kuma Sani Gurgu.
Daga yankin Arewa maso gabas kuwa, hedkwatar na neman mutane 33 wanda mayakan boko haram da na kungiyar ISWAP ne.
Inda mutanen suka hada da Ali Ngule, Abu Zaida, Modu Sulum, Baba Data, Sani Teacher, Baa Sadik, Abdul Saad, Kaka Abi, Khalifa, Umar Tella, Abu Mutahid da dai sauransu.
Hedkwatar ta ce daga yankin kudu maso gabas kuwa da Arewa ta Tsakiya tana neman ‘yan tada kayan 21 a yankunan.
Mutanen suna Simon Ekpa, Chika Edoziem, Zuma, Gentle, Flavour, High Chief, Friday Ojimka da dai sauransu.