Hukumar aikin hajji ta ƙasa Najeriya ta ƙara naira miliyan 1.9 a kan kuɗin da aka ƙayyade na naira 4.9 da za a biya kuɗin aikin hajjin bana.

Hakan na ƙsunhe a wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Lahadi, mai ɗauke das a hannun Fatima Sanda mai Magana da yawun hukumar.
An ƙara kuɗin ne kwatam, yayin da su ka tsayr da ranar 28 ga watan Maris ɗin da mu ke ciki a matsayin ranar ƙarshe don biyan kuɗin ga maniyyata.

Hukumar ta buƙci waɗanda su ka biya kuɗin da farko na naira miliyan 4.9 da su ƙara naira miliyan 1.9 don su zama naira miliyan 6.8 kafin samun dammar zuwa iadar.

Hukumar ta buƙaci maniyyatan da su ziyarci hukumar aikin hajji ta jihohinsu domin sanin matsayinsu kan tafiyar.
Hukumar ta yabawa ƴan ƙsar a kan yadda su ke nuna tsantsar fahimta a garesu tare da bayar da haɗin kai, wanda su ka ce hakan ma ya faru ne saboda wasu dalilai.