Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Ganduje ya ce sam bai girgiza ba kuma har yanzu ya na nan dara matsayin shugaban jamiyyar na ƙasa.

A wani bidiyo da ya  ke yawo a kafofin sa da zumunta, Ganduje ya zargi gwamnatin Kano da jam’iyyar NNPP da hannu a abinda ya kira maƙarƙashiya da aka yi masa kan batun dakatar da shi daga cikin jam’iyyar daga matakin mazaɓa.

Ganduje ya ce ya gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kuma ya tabbatar masa da cewar har yanzu shi ne shugaban jam’iyyar APC.

Wannan na zuwa ne bayan da wani ɓangare na shugabancin  jam’iyyar a mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawain Tofa su ka sanar da dakatar da shi daga cikin jam’iyyar.

Sai dai a wani bidiyo da aka gano shugaban jam’iyyar na mazaɓar ya ce ba da aywunsu wannan sanarwa ta fita ba, kuma waɗanda su a fitar da sanarwa ba sa tare da su.

An fara wanan sa toka sa katsin ne tun bayan da kotun ƙoli ta tabbatar da Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin halastaccen gwamnan Kano.

A ƴan kwanaki nan dai gwamnatin Kano ta shugar da ƙara a gaban kotu wanda take zargin tsohon gwamnan Abdullahi ganduje da yin almundahana, aiwatar da gwamnati  a yadda ya kamata ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: