Mutane 13 ne su ka mutu yayin da wasu su ka jikkata a sakamakon wani hatsari da ya auku a jihar Kogi.

Lamarin ya faru a jiya Lahadi wanda ya haɗa da wata mota kirar Bas da wata Hayis wadda ta taso daga Abuja ta nufi Fatakwal.


Wani da al’amarin ya faru a gabansa ya ce motocin biyu na daukar fasinja sun yi taho mu gama.
Ya ce mutane 13 ne su ka mutu ciki har da direban motar hayis kuma nan take su ka kama da wuta.
Sai dai wani daga cikin mutanen da lamarin ya rutsa da su ya mutu ne bayan da aka kaishi asibiti.
Yayin da mutane 10 daga ciki kuwa su ka jikkata da samun munanan raunin.
Bayan da lamarin ya faru, mutanen kauyen da ke kusa sun ka musu dauki wanda hakan ya sa aka tseratar daa wasu daga ciki.
Yayin da aka tuntuɓi kwamandan hukumar a jihar ya tabbatar da faruwaar lamarin, sai dai ya ce bai samu cikakken bayani a kai ba.