Rundunar sojin Najeriya ta kori wasu jami’an ta biyu bayana da ta samesu da laifin aikata fashi a matatar mai ta Ɗangote a jihar Legas.

 

Bayan bincike da aka yi an kori Innocent Josep da Jacob Gani waɗanda aka zarga da satar wata waya a matatar.

 

A ranar 14 ga watan Afrilu ne dai aka samu mutanen da aikata satar wanda aka samu wayar lantarki mai yawa.

 

Yayin da yake tabbatar da korar jami’an yau Litinin Onyema Nwachukwu mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, ya ce an samu jami’an biyu da aikata laifin.

 

Bayan samunsu da aikata laifin, tuni aka sallamesu daga baki aikin kadar yadda dokar aikin ta yi tanadi.

 

Ya ce hukumar su ba za ta lamunci rashin ɗa’a da sabawa dokar aikin soja ba.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: