Sufeton ƴan sanda na ƙasa Kayode Egbetokun ya ce Najeriya ba ta cancanci samar da ƴan sandan jihohi ba.

 

Kayode ya bayyana haka ne a wajen taron baje kolin ra’ayi dangane da baiwa jihohi damar samar da ƴan sandansu.

 

A kwanakin baya dai kun ji yadda mu ka baku labari wanda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da batun kafa ƴan sandan jihohi a Najeriya bayan da gwamnoni su ka sha kiraye kiyaye a kai.

 

A wajen taron da aka yi yau a Abuja, sufeton ƴan sandan wanda mataimakinsa Ben Okolo ya wakilta, ya ce a maimakon samar da ƴan saandan jihohi kyuatuwa ya yi a haɗe hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC, da hukumar kiyaye afkuwar haddura FRSC don ganin sun koma ƙarƙashin jami’an yan sanda.

 

Sannan a ƙara yawan ɗaukar jami’an yan sanda zuwa 30,000 maimakon 10,000 da ake yi.

 

Wannan shi ne tsarin da ya yi daidai da tsarin majalisar ɗinkin duniya dangane da ɗaukar mafi karancin yan sanda a kasashe.

 

Idan za a iya tunawa, wasu gwamnoni a Najeriya sun yi ta kira a baya don ganin gwamnatin tarayya ta sahale musu don samar da ƴan sandan jihohi, domin magnace matsalar tsaro da ta addabi jihohin.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: