Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN), ya tabbatar da cewa bata gari sun lalata turakun wayar lantarki guda hudu da ke rarraba wutar lantarki a hanyar Jos zuwa Gombe.

Lalata turakun layukan wutar ya janyo an fada cikin rashin wutar lantarki a jihohi uku da suka hada da Adamawa, Gombe da Taraba.
Manema labarai sun ruwaito jami’in hulda da jama’a na TCN, Ndidi Mbah, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Litinin.

Sakamakon haka, wutar lantarki a tashoshin Gombe, Yola, da Jalingo su ka sami matsala, lamarin da ya yi illa ga yawan wutar lantarkin da kamfanonin rarraba wutar na Yola da Jos ke samu.

Ya ce, kamfanin TCN ya na sanar da cewa an lalata turakun hudu da ke dauke da manyan layukan rarraba wutar lantarki ta hanyar Jos zuwa Gombe mai karfin kilo 330kV da misalin karfe 3:32 na yammacin yau 22 ga Afrilu, 2024.
A yayin wani rangadi ne injiniyoyin TCN suka gano cewa an lalata turaku na 288, 289, 290, da 291 kuma an datse layukan wasu hanyoyin, wannan tasa sun daina aiki gaba daya.