Shugaba Bola Tinubu zai halarci taron tattalin arzikin duniya da aka shirya gudanarwa a ranakun 28 zuwa 29 ga watan Afrilu a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.

A wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Litinin, ya ce, bisa gayyatar da Firaministan Netherlands, Mark Rutte ya yi masa.


Yayin ziyarar, shugaba Tinubu zai tattauna da Firaministan, sannan zai shiga taruka daban-daban tare da Mai Martaba, Sarki Willem-Alexander da Sarauniya Maxima ta Masarautar.
Har ila yau a yayin da ya ke kasar Netherlands, shugaba Tinubu zai halarci taron kasuwanci da zuba jari a tsakanin Najeriya da Netherlands wanda zai hada shugabannin kungiyoyi a kasashen biyu don gano damarmaki na hadin gwiwa.
Ya ce musamman a fannin noma da kula da ruwa wajen samar da sabbin hanyoyin samar da mafita mai dorewa ga ayyukan noma.
Za kuma a tattauna da jami’an kasar game da ayyukan sarrafa tashar jiragen ruwa wadanda a duniya an san su da kwarewa a kai.