Jami’an yan sanda a Jigawa, sun kama wani Adamu Bello mai shekaru 56 a karamar hukumar Buni Yadi a jihar Yobe.

 

An Kama shine da laifin hada baki, sacewa da kuma kisan gilla na wani Abdullahi Adamu mai shekaru 30 a kauyen Musari, da ke karamar hukumar Guri.

 

An kama wanda ake zargin ne a kauyen Maimari na jihar Yobe.

 

Jami’an sun samu korafin a ranar 28/06/2023 ga ofishin kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa a rubuce cewa, a ranar 24/06/2023 da misalin karfe 1:20, wasu gungun mutane da har yanzu ba a tantance ba, sun kai kimanin 12, dauke da bindigogi da wasu muggan makamai sun shiga gidan wani Abdullahi Adamu mai shekaru 30 a kauyen Musari da ke karamar hukumar Guri, suka yi awon gaba da shi.

 

Bayan samun rahoton, jami’an tsaro na hukumar leken asiri ta jihar Dutse (SID) sun shiga aikin bincike, inda jami’an su ka kama mutane hudu da ake zargin da hannunsu a ciki.

 

Daga cikin wadanda aka kama akwai Buba A. Abdu mai shekaru 37, mazaunin Guri LGA, Bello Mallam mai shekaru 20 na Mamadaku ƙauyen Birniwa LGA, da Adamu Dahiru mai shekaru 28 na Maje garin Auyo LG da Mamman Bille mai shekaru 30 na Bodala a kauyen Guri LGA.

 

‘Yan sanda sun ziyarci wurin da lamarin ya faru a kauyen Maina Daku na karamar hukumar Birniwa.

 

A yayin da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa cewa sun hada baki da Adamu Bello wajen aikata laifin.

 

Sannan bayan karbar kudi naira miliyan uku a matsayin kudin fansa, sun kuma kashe wanda aka sace.

 

Adamu Bello ya kuma bayyana cewa an ba shi Naira dubu dari biyu da goma daga kudin fansar da aka karba.

 

Har ila yau rundunar ta kuma kama, yan fashi da makami, masu karya suna garkuwa da mutane, masu saida miyagun kwayoyi, da manyan masu laifuka daban daban.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: