Wasu da ake zargi masu garkuwa ne sun kashe mutane uku tare da yin awon gaba da wasu Takwas a jihar Kaduna.



Lamarin ya faru a ƙauyen Hayan Habuja da ke gujdumar Kakangi a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar.
Wannan na zuwa ne kwana biyar bayan da ƴan bindiga su ka kashe mutane 23 a Anguwan Danko kusa sa garin Dogon Dawa a ƙaramar hukumar Birnin Gwari.
An kashe mutanen a jiya Talata da misalin ƙarfe 03:00pm na rana kamar yadda shugaban ƙungiyar masarautun Birnin Gwari Abdurrashid Abarshi ya bayyanawa gidan talabiji na Channels.
Ya ce an harbe mutane biyu kai tsaye a wajen yayin da su ka tafi da mutane huɗu.
Ya ƙara da cewa yayin da ƴan bindgan ke kan hanyarsu ne a ƙauyen Hayin Habuja su ka sake awon gaba da wasu mutane huɗu bayan sun kashe mutum guda
Ya ce waɗanda aka tafi da su a kan hanyar sun dawo ne daga yin itace a daji.
Ko da aka tuntuɓi jami’an yan sanda a jihar dangane da faruwar lamarin, ba su ce komai a kai ba.