Rundunar sojin saman Najeriya ta samu nasarar hallaka yan ta’adda da dama a wani aikin haɗin gwiwa da su ja yi ƙarƙashin Operation Haɗin Kai.



A wata sanarwa da ta fitar yau Laraba, rundunar ra ce ta lalata maɓoyarsu a ƙananan hukumomin Damasak da Mobbar a jihar Borno.
Mai magana da yawun sojin saman Najeriya Edward Gabkwet ya ce ƴan ta’addan na shirin kaiwa jami’an hari a Lada iyaka da e tsakanin Najeriya da Nijar.
Ya ce maharan na kan hanyar tasu kan babura ne kuma aka gano maɓoyarsu a wasu wuri biyu na kauyen Zarri nisan kilomita 28 zuwa ƙaramar hukumar Damasak da Mala a ƙaramar hukumar Mobbar.
Bayan bibiyarsu da aka yi su ka ahirya tawaga ƙarƙashin Operation Haɗin Kai a jiya Talata.
Bayan hallakasu ne kuma su ka lalata sansanin da su ke shirin kafawa
Hukumar ta gano cewar maharan sun ketaro ne daga ƙasar Nijar da nufin kafa sansani a yankunan da aka cimmusu