Hukumaar kiyaye afkuwar hadduta ta kasa aa Najeriya FRSC ta ce an samu raguwar haddura da kashi 42 la’akari da yadda ake samun hadduran a baya

Shigaban hukumar na ƙasa Dauda Biu ne ya bayyana haka a Abuja.


Ya ce mayar da hankali wajen tabbatar da bin kaidar tuki ya taimaka matuka wajen raguwar haddura da ake samu
A cewarsa, ko da a bikin salla karama da aka gaabatar a baya bayan nan,an samu raguwar haddura wanda hakan ya rage yawan mutanen da ke mutuwa.
Dangane da mutanen da ke mutuwa a lokutan bikin salla, an samu raguwarsu da kashi 52.5.
Yayin da aka samu raguwar mutanen da aka tseratar ba tare da rauni ba da kashi 43.8
Su kuwa mutanen da su ke samun rauni an samu ragi daa kashi 32.6, yayin da aka samu raguwar hadduran da kashi 42.5 la’akari da shekarar da ta gabata.
Sannan an samun raguwar masu karya dokokin tuki da kashi 14.5.