Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar kama wasu masu garkuwa biyu, yayin da au ka dakile wasu hare-hare a jihohin Sokoto, Kaduna da Filato.

Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da su ka wallafa a shafinsu na X wato Twitter.


Su ka ce sun samu nasara ne a jiya Laraba.
Sanarwar ta ce sun tarwatsa ƴan bindigan a kauyen Sarma da ke Tangaza a jihar Sokoto.
Bayan wuta da su ka buɗe musu sun kuma babur, harsashi, da bindiga kirar AK47 guda ɗaya.
A wani cigaban kuma jami’an sun daƙile wani hari a hanyar ƙauyen Kasu da ke Kafanchan a karamar hukumar Jema’a a Kaduna.
A wannna waje ma sun kwato babur guda, harsashi da sauran makamai sannan su ka kama mutane biyu da su ke zargi masu garkuwa ne.
A wani farmakin da su ka kai a jihar Filato, a ƙaramar hukumar Barikin Ladi sun kashe ɗan fashi guda a shingen bincike da ke Kaskara.