Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta yi karin haske kan wani faifayin bidiyo da ke yawo da kan cewa an kai hari kan masu ababen hawa a birnin tarayya Abuja.

Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook. Rundunar ta ce bayan binciken da ta gudanar ya nuna cewa faifayin bidiyon an yi shi ne a Kasar Habasha ba a birnin tarayya a Abuja ba.
Rundunar ta kara da cewa wani mutum ne ya tura bidiyon a shafinsa na X inda ya ke yawan korafi a kan yawaitar kai hare-hare a Kasar ta Habasha.

A cewar rundunar bayan fitar da bidiyon da mutumin ya yi wasu mutane suka dauka tare da yadawa kan cewa an kai harin ne a birnin na Abuja.

Rundunar ta kara da cewa bayan kammala binciken shugaban ‘yan sanda na Kasa Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin yin cikakken bincike a kan wadanda suka yada cewa a birnin Abuja aka kai harin.
A cewarta da zarar an kama wadanda ake zargin hukumar za ta dauki mataki akan abinda suka aikata.
Sannan rundunar ta ce za ta ci gaba da sanya idanu akan masu aikata irin wadanda miyagun laifuka a shafukan sada zumunta domin kamosu tare da hukuntasu.