Bayan kai ruwa rana da ake yi tsakanin Tsohon gwamnan Jihar Kogi Yahya Bello da hukumar yaki da masu yiwa tattain arzikin kasa zagon kasa ta EFCC kan badakalar wasu kudade wata Makarantar kasa-da-kasa ta Amurka da ke birnin tarayya Abuja AISA ta ce za ta mayar da kudin makarantar dan tsohon gwamnan Yahaya Bello da ya biyawa dan nasa.

A wata wasikar da hukumar makarantar ta aikawa da EFCC ta nemi da a basu bayanan asusun bankin hukumar domin su tura mata kudaden.

Makarantar ta ce Yahaya Bello ya tura mata dala 845,852 na kudin makarantar yaransa har zuwa lokacin da zai kammala karatun a makarantan.

Rahotannin sun bayyana cewa dan tsohon gwamanan na Kogi a halin yanzu na a matakin aji na 2 a makarantar.

Makarantar ta aikewa da hukumar shiyyar Jihar Legas wasikar, inda ta bayyana cewa Yahya Bello ya tura mata kudaden makarantar yaron nasa ne tun a ranar 7 ga watan Satumba 2021 da ta gabata.

Amma makarantar ta bayyanawa EFCC cewa dala 760,910 kadai za ta turawa hukumar saboda ta cire kudaden da yaron yayi karatu zuwa yanzu .

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: