Kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya ki karbar kudirin da aka gabatar na bukatar dakatar da harajin tsaron yanar gizo.

Manema labarai sun ruwaito cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya umarci dukkanin bankunan kasar da su fara cire 0.5% daga hada-hadar kudaden abokan hulda daa aka yi ta yanar gizo.


Kungiyar kwadago ta yi watsi da wannan harajin, inda ta bayyana shi a matsayin wani karin nauyi a kan ‘yan Najeriya.
A zaman majalisar na ranar Laraba, dan majalisa Manu Soro daga jihar Bauchi ne ya gabatar da kudirin, inda ya nuna damuwarsa kan yadda harajin zai kara jefa mutane a matsin tattalin arziki.
Soro ya kara da cewa kakaba sabon haraji a wannan yanayi na kalubalen tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta, zai kara jefa ‘yan kasar cikin tsadar rayuwa da tsadar abinci.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Soro ya yi kira ga majalisar da ta tilastawa banki CBN ya janye daftarin harajin tsaron yanar gizo tare da dakatar da aiwatar da shi cikin gaggawa.