Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika, ɗiyarsa, da wasu mutane biyu.

Kotun ta ba da belin kowanne mutum daya a kan kudi Naira miliyan 100 kuma za su gabatar da mutum biyu-biyu da za su tsaya masu.

An gurfanar da su a gaban kotun ne bisa tuhumar zargin zamba ta Naira biliyan 2.7.

A cewar kotun, dole ne ya zamana wadanda za su tsaya masu sun mallaki kadarori a Abuja da kuma zama ‘yan kasa na gari.

Waɗanda za su tsayawa wadanda ake ƙarar za su gabatar takardar shaidar kadarori da dukkanin abubuwan da kotun take bukata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: