Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane tare da satar shanu a kauyen Gidan-Maga da ke cikin karamar hukumar Malumfashi ta Jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘ƴan sandan Jihar Abubakar Sadik Aliyu ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Kakakin ya ce nasarar ta samu ne bayan wani kiran gaggawa da jami’ansu suka samu akan ‘yan ta’addan na yunkurin kai harin.

Aliyu ya kara da cewa jami’ansu da ke garin Malumfashi a Jihar ne suka samu bayanai akan ƴan bindigar dauke da makamai sun yi garkuwa da mutane goma tare da shanu 16 a kauyen.

Ya ce bayan samun bayanan baturen ‘yan sandan yankin ya aike da jamiansu garin ,inda suka yi musayar wuta da ‘yan bindigar kafin daga bisani su ceto mutanen tare da shanunsu.
Sadik ya ce a yayin musayar wutar ‘yan ta’ddan sun tsere dauke da raunuka a tare da su.
Bayan samun nasarar Kwamishinan ‘yan sandan Jihar CP Aliyu Abubakar Musa ya jinjina tare yabawa jami’annasu bisa nasarar da suka samu akan ‘yan ta’addan.
Sannan kwamishinan ya bayyana cewa za su ci gaba da kara kaimi wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyooyin al’uummar Jihar ta Katsina.