Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a birnin tarayya Abuja ta ki amincewa da bukatar janye kama tsohon gwamna Kogi Yahaya Bello.

Alkalin kotun mai shari’a Emeka Nwite ne ya ki amincewa da bukatar bayan gabatar da bukatar janye umarnin janye kama tsohon gwamnan a gaban kotun.
Alkalin ya bayyana cewa dakatar da kama tsohon gwamnan na kogi wani yunkuri ne na kawo cikas ga karar da hukumar EFCC ta shigar a kansa.

Alkalin ya kara da cewa ya zama wajibi Yahya Bello ya bayyana agaban kotu domin amsa tambayoyi akan zarge-zargen da hukumar EFCC ta ke yi masa nayin sama da fadi da wasu kudade.

Alkalin ya ce tunda Yahaya Bello ya ki bin umarnin kotun ba za a bari ya kara shigar da wata kara gaban wata kotun ba kuma ba za a saurare shi ba.
Alkalin ya ce ko da ba a bi ka’ida ba wajen kama Tsohon gwamnan, dole ya bayyana a gaban kotun domin kalubalantar hakan.
Alkalin ya bayyana hakan ne bayan da tsohon gwamna na kogi ya roki kotu kan ta dakatar da sauraron karar da hukumar EFCC ta shigar a kansa har sai kotun daukaka kara ta yanke hukunci akan makamanciyar irin karar da ta shigar.