Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta takaice tsare-tsare da aka saba yayin da ake gab da shekara guda, karkashin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ministan yada labara a Najeriya Mohammed Idris ne ya bayyana haka ya ce za a takaita al’amura gudanarwar ne duba ga halin da kasar ke ciki na matsin tattalin arzki.
Ministan wanda ya bayyana hakan yau cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labara, ya ce yana daga cikin tsari da manufofin shugaba Bola Tinubu sassauci da kuma yin abinda zai dadada ran yan kasar.

Ya ce ba za a yi biki cika shekara ba kamar yadda aka saba a gwamnati, illa su umarci ma’akatu domin bayyanar da ayyukan da su ka yi.

Wannan kuma mataki ne da gwamnatin ta dauka domin rage yawan kashe kudadi bisa halin da kasar ke ciki.
Tuni shugaban ya bayar da umarnin ga ma’aikatun da su fitar da bayanai na gaskiya kuma masu ma’ana cikin furuci mai kyauwu.
Sannan ya bukaci yan jarida da su ruwaito labarai na gaskiya musamman a kan yadda za a fitar da ayyukan da gwamnatin ta yi cikin shekara guda.