Shugaba Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin siyan kayan abinci da su ka kai naira biliyan 155 tare da rabawa a ƙasar.

Tinubu ya amince da wannan batu ne yayin zaman majalisar tattalin arziki da ya gudana a ranar Alhamis.


Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci gwamnonin jihohi su ba da haɗin kai don ganin kayan ya isa ga mabukata a jihar
Ya ce burinsa bai wuce samar da hanyar da za a ragewa ƴan Najeriya raɗaɗi halin da su ke ciki ba.
Sai dai a zaman da aka yi na majalisar tattalin arziki ba a tattauna batun mafi ƙarancin albashi ba.
Batun da a baya ake zargi na daga gaba gaba da za a tattauna a zaman da aka yi.
Tinubu ya zauna da gwamnoni da mataimakansu, ministoci da sauran masu ruwa da tsaki don tattauna lamuran da su ka shafi tattalin arziki.