Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya roki matasan ƙasar da su jingine batun zanga-zanga tare da ƙara bashi lokaci

 

Ministan yaɗa labarai a Najeriya Mohammed Idris ne ya bayyana haka yau yayin ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa.

 

Ya ce shugaba Tinubu ya bashi unarnin ganawa da ƴan ƙasar musamman ma matasa dangane da batun zanga-zanga da su ke shiryawa

 

Ya ce a halin da ake ciki su na kan ɗaukar matakan da za u bi don ganawa da masu shirya zanga-zangar.

 

Ministan ya ce sun gana shugaban ƙasa kuma ya yi masa dukkan bayanan matsalolin da ake fuskanta

 

Sannan ya ce a halin yanzu shugaban ƙasar na aiki haikan don ganin komai ya tafi cikin hanzari yadda za a samar da mafita ga matsalolin.

 

Ministan ya ce shugaban ya buƙaci a sake bashi lokaci domin ganin irin tanadin da ya yi wa ƴan kasar a kan koken da su ke yi

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: