Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da kaddamar da fara aikin ginin titin Dorayi zuwa Panshekara a Jihar.

Hadimin gwamnan Jihar na musamman da ke kai masa bayanai daga ma’aikatar ma’aikatun jihar Khamis Bashir Bako Ayagi ne ya bayyana hakan ta cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook jiya Asabar.

Sanarwar ta ce gwamna Abba ya kuduri aniyar kammala aikin hanyar ne sakamakon gazawar da gwamnatin tarayya ta yi wajen karasa aikin titin.

Sanarwar ta kara da cewa an gaza kammala aikin titin ne tun a zamanin tsohon shugaban Kasa Muhammad Buhari, wanda hakan ke haifa da kalubalai ga mazauna yankin da kuma masu bin hanyar.

Ayagi ya ce gwamnatin ta Kano za ta kammala aikin titin ne bayan yawaitar kiraye-kirayen da mazauna Jihar ke yi kan rashin kammala aikin na gwamnatin tarayya.

Wanda hakan ya sanya gwamnatin Jihar ta duba korafe-korafen jama’a da kuma inganta harkokin sufuri a Jihar, wanda hakan ya sanya ta dauki matakai domin ganin an magancewa mazauna yankin Matsalar, tare da samar musu da ababan more rayuwa.

Ayagi ya ce a yayin ci gaba da gudanar da aikin kwamishinan ayyuka da gidaje na Jihar Injiniya Marwan Ahmad Aminu ya kai ziyara gurin, domin ganin yadda aikin titin ke gudana.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa gwamnatin Jihar ta kuduri aniyar samar da ingantattun kayayyakin more rayuwa da za su amfanar da al’ummar Kano baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: