Ƙungiyar dilallan man fetur a Najeriya IPMAN ta zargi kamfanin mai na ƙasa NNPC dangane da tsadar man da ake ciki a yanzu.

Ƙungiyar ta ce ba ta smaun isashen mai daga kamfanin wanda hakan ya haifar da ƙarancinsa.
Ta ce akwai mambobi sama da 3,000 a waɗanda e ƙoƙarin gani sun wadata ƙasar daman fetur ɗin da ake buƙata sai dai ba sa samun isashen man daga kamfanin mai na ƙsa.

A wata zantawa da aka yi da shugaban ƙungiyar dilallalan man ta ƙasa Injiya Shina Amoo yau Talata, ya ce fiye da shekara uku kenan ba sa samun isashen mai daga kamfanin mai na ƙsa NNPC.

A cewarsa, kamfanin NNPC na siyarwa da wasu masu zaman kansu mai a kan kuɗi naira 560, sannan su kuma su siyarwa da dillalan man a kan kuɗi naira 800, 850, zuwa 870.
Ko da cewar bai ambaci sunayen waɗanda ake siarwa daman ba, amma ya ce fiye da shekara uku kenan su na cikin wannan yanayi
A wasu jihohi a Najeriya dai ana siyar da itar mai a gidajen mai naira 1,000 kan kowacce lita, wanda hakan ke ƙara barazana ga farashin kayayyaki a ƙasar.