Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce ta samu nasarar tseratar da dukiyar da ta ki naira miliyan 102,950,000 a watan Agusta.

Mai magana da yawun hukumar Saminu Yusuf ne ya bayyanawa Matashiya TV haka a yau.

Ya ce gobara ta laƙume dukiyar da ta kai naira miliyan 47,800,000.

Sannan a watan da ya gabata an samu rasuwar mutane uku sannan an tseratar da rayukan wasu mutane uku.

Ya ce sun samu kiran ceto guda 11 yayin da su ka samu kira kn tashin gobara gida 21.

Shugaban hukumar Hassan Ahmad Muhammad ya ja hankalin al’ummar jihar da su dinga kiyaye dukkanin wata hanya ta afkuwar gobara.

Sannan ya ja hankalin dorebobi dasu dinga bin dokokin tuki dokin kiyaye asarar rayuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: