Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe wato Grassroot Care and Aid Foundation GCAF ta yi Kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta janye ƙarin kuɗin da NNPCL ta yi a wannan yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa wanda asalinsa dama janye tallafin man fetur da aka yi shine sanadin hakan.

Shugaban Gidauniyar Amb. Auwalu Muhd Danlarabawa shine ya bayyana hakan yau ga manema labarai domin nuna damuwa da halin da al’umma ke ciki na tsadar rayuwa da hauhawar farashi dama yawan Mutuwa da ake tayi sanadin rashin abinci.
Amb Auwalu Muhd Danlarabawa ya Kara da cewa wajibi ne Yan majalisu suyi wani Abu akan wannan al’amari dare da Gwamnonin da suke Jagorancin al’ummar kasa indai da gaske suke dimokradiyya ake yi.

Idan har baa dauki mataki ba a wannan yanayi to gaskiya alama ta nuna cewar shugabannin da muke dasu ba Imani da tausayin al’ummar kasa a tare dasu.

Sannan ya Kara da kira ga ƴan kwadago da su yi abinda ya dace a wannan gaba na kira da a janye ko Kuma a tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.