Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya NDLEA reshen jihar Kano ta musanta labarin da ake yaɗawa cewar ta samu ƴan takarar shugabannin ƙananan hukumomi da ke ta’ammali da kayan maye.

Mai magan da ya yawun hukumar Sadik Maigatari ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya aikewa da Matashiya TV.

ya ce ba a fahimci bayanin shugaban nasu ba, a cewarsa hukumar ta fara aikin tantance ƴan takarar shugabannin ƙananan hukumomin kuma ta na ci gaba da aikin tantancewar.

Maigatari ya ce akwai ƴan takarkarun kansila da shugabannin ƙananan hukumomi da hukumar ke tantancewa kuma zuwa yanzu an tantance sama da mutane 300.

Hukumar ta buƙaci jama’a da su yi watsi da labarin su na masu cewar ba su fayyace waɗanda ke neman shugabancin ƙananan hukumomi d kansila waɗanda ke shan ƙwaya ba.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar Kano ce dai ta haɗa kai da hukumar ta NDLEA domin tantance ƴan takarar shugabannin ƙananan hukumomi da kansila gababin zaɓen da za a yi a nan gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: