Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya ce shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da mashaawarcinsa kan sha’anin tsaron ƙasa na da masaniya kan zargin tsohon gwamnan kuma ƙaramin ministan tsaro Muhammad Bello Matawalle da alaka da yan bindiga.

Gwamnan ya ce ya gabatarwa da mashawarcin shugaban kasa kan tsaron kasar Malam Nuhu Ribadu korafi da hujjoji kan zargin


Yayin da yake ganawa da gidan talabiji na Channels, Matawalle ya ce kalubalanci gwamnan da Janar Aliyu Gusau mai ritaya da su rantse da Alkur’ani idan ba su da hannu a matsalar tsaron jihar da arewa maso yammacin ƙasar.
Matawalle ya ce zangin da ake masa na ɗaukar nauyin taaddanci ba shi da tushe.
Haka kuma tattaunawar da yake yi da ƴan ta’adda ya na yi ne domin a daina kashe-kashe.
Kuma irin wannan tattaunawar gwamnonin Katsina, Sokoto da Neja sun yi irinta
Da ya ke mayar da martani dangane da batun, babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Zamfara Sulaiman Idiris ya ce akwai kwararan hujjoji da su ke da shi kuma za su raba ga manema labarai ba da jimawa ba .
Kuma ya tabbatar da cewar gwamnan ya yi rantsuwa da Alkur’ani tare da addu’ar Allah ya hukunta dukkan mai hannu a sha’anin ta’addacin da ake yi.