Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta wanke Alhassan Ado Doguwa daga zargin kisan kai da gwamnatin Kano ke yi masa a zaben 2023 da ya gabata, tare da haramtawa gwamnatin Jihar kamashi da kuma cin zarafinsa.

Kotun karkashin Mai Shari’a Donatus Okorowo ne ya yanke hukuncin, tare da bai’wa gwamnatin umarci biyan Doguwa diyyar kudi har na Naira miliyan 25.

Sannan kuma Kotun ta yi watsi da korafe-korafen da gwamnatin jihar ta shigar gabanta kan Doguwa bisa zarginsa da laifin aikata zargin kisan kai a zaben 2023.

Doguwa ya ce korafin da aka shigar game da shi kan takardamar zaben 2023 an gudanar da bincike kuma jami’an ‘yan sanda da babbar kotun jihar Kano sun wanke shi.

Sannan Doguwa ya mika godiyarsa ga Allah bisa nasarar da ya samu a gaban kotun kan zargin da ake yi masa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: