Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta kama wani magidanci mai shekaru 30 a duniya mai suna Motunrayo Olaniyi da hallaka sabuwar matarsa mai suna Olajumoke mai shekaru 25 ta hanyar caka mata wuka da yayi.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar.
Kakakin ya bayyana cewa mutanen ya yi aika-aikar ne a jiya Juma’a ta 4 ga watan Oktoban nan a yankin rukunin gidaje na Amazing Grace da ke Elepe a yankin Ikorodu na Jihar ta Legas.

Benjamin ya ce lamarin ya faru ne bayan wani rikici ya barke a tsakaninsu, wanda hakan ya sanya magidanci ya cakawa amaryar tashi wuka, tare kuma da kulle ta a cikin daki, daga bisani ya sanya mata wuta.

Kazalika Kakakin ya ce magidancin ya kuma jikkata kansa a yayin rikicin.
Benjamin Hundeyin ya kara da cewa jami’ansu da suka isa gurin ne suka kashe wutar da mutumin ya kunna, tare da gano gawar matar.
Jami’in ya ce rundunarsu ta samu labarin faruwar lamarin ne bayan wani kira da suka samu, inda kuma aka kai mutumin Asibiti bisa raunukan da ya samu, daga bisani kuma aka sallame shi sannan jami’an ’yan sanda suka tsare shi.
Kakakin ya ce a halin yanzu an ajiye gawar matar a ɗakin ajiye gawarwaki na babban asibitin Ikorodu domin ci gaba da gudanar da bincike.