Gwamnatin tarayya ta amincewa gwamnatin Jihar Kogi da ta gina filin sauka da tashin jiragen sama na Kasa da Kasa a Jihar.

Kwamishinan yada labarai da sadarwa na Jihar Kingsley Fanwo ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a.

Sanarwar ta ce ma’aikatar sufurin jiragen sama ta tarayya cewa, ta amincewa da aniyar gwamnatin ta Kogi, ta cikin wata takarda da ta fitar mai dauke da kwanan watan 9 ga watan Oktoban nan.

Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin Jihar karkashin jagorancin gwamna Usman Ododo ta mayar da hankali domin ganin ta kammala aikin ginin filin jiragen saman a kan lokaci.

Fanwo ya ce filin jirgin saman da za a gina a Jihar ta Kogi na da girma kuma Jihohi Goma suma za su iya amfana da shi, kuma zai rage yawan zirga-zirgar ababen hawa a hanyar Lokoja zuwa birnin Abuja, kuma zai kawo karshen cikowar da ake samu a filin jirgin saman Abuja.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: