Babbar Kotun Jihar Kano ta bai’wa hukumar zabe mai zaman kaanta ta Jihar Kano KANSIEC umarnin gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomin a gobe Asabar.

Alkalin kotun Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji ne ya bai’wa hukumar umarnin a zaman da kotun ta gudanar a safiyar yau Juma’a.
Ma’aji ya yanke hukuncin ne bayan da hukumar ta KANSIEC ta shigar da kara gabanta, bayan da babbar kotun tarayya ta dakatar da hukumar daga gudanar da zaben, tare da kalubalantar jam’iyyar APC da wasu mutane 13, da ke neman dakile hukumar ta gudanar da zaɓen.

Sannan Alkalin ya kuma umarci jami’an tsaron ‘yan sanda da su bayar da tsaro a lokacin zaben, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yayin zaben.
