Kungiyar dattawan arewa ta sake kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta janye kudirin sauya fasalin dokar haraji.

Karo na biyu kenan da kungiyar dttawan ta yi wannan kira tun bayan da gwamnatin tarayya ta yi yunkurin sauyawa dokar fasali.

A wata sanarwa da ƙungiyar dattawan ta fitar jiya Asabar mai dauke da sa hannun shugaban gudanarwa Al Amin Daghash, sanarwar ta ce fasalin harajin da ake ƙoƙarin yi na iya taba yankin arewa da ma ƙasa baki ɗaya.

Sai dai kungiyar ta ce ba ta adawa da tsarin da zai kawo ci gaba ga arewa da ma kasa baki daya.

Tun da farko dai kungiyar dattawan arewan ta yi watsi da kudirin sauya fasalin harajin da gwamnatin tarayya ta bijiro da shi.

Haka ma gwamnonin arwacin ƙasar sun soki batun

Ko a ranar Laraba sai da gwamnatin Kano ta sake fitowa karara ta nuna cewar ba ta tare da tsarin da gwamnatin ke son yi a ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: