Helkwatar tsaro a Najeriya ta ce ta na duba yiwuwar samar da bangaren hada makamai na gida a ƙasar.

Babban hafsan tsaro a Najeriya Janar Christopher Musa ne ya bayyana haka yayin da ya ziyarci dakarun Operation Safe Haven a jihar Filato.
Ya ce su na shirin karawa jami’an kayan yaki da su ka hada da makamai da motoci da kuma kula da walwalarsu

Haka kuma ya bukacesu da su kara kaimi wajen fatattakar ƴan ta’adda tare da zakulosu a ko ina su ke a maboyarsu.

Janar Musa ya duba wasu daga cikin makamai da aka kama waɗanda aka sarrafa a cikin gida.
Sakamakon haka ya nuna bukatar samar da bangaren sarrafa makamai a bangaren sojin.
Janar Musa ya bukaci jami’an da su kasance masu mutunta dan adam sannan ya yaba musu bisa ƙoƙarin da su ke yi