Jami’an sojin Najeriya sun hallaka fitacce ɗan bindiga Sani Rusu a jihar Zamfara.

 

Jami’an tawagar Operation Fansar Yamma ne su ka hallaka fitaccen dan bindigan kamar yadda mai magana da yawun tawagar Abubakar Abdullahi ya shaida.

 

Ya ce an hallaka shi a ƙauyen Bamamu d ake ƙaramar hukumar Tsafe a jihar.

 

Sannan sun kai masa hari ne bayan samun bayanan sirri a kansa.

 

Haka kuma jami’an sun hallaka wasu da yawa daga yan bindigan yayin daa wasu su ka jikkata.

 

Jami’an sun kwaato jindiga kirar AK47 guda daya da wasu makamai.

 

A wani hari da tawagar da ke yaki ta sama au ka kai tsakanin Fakai da Kware a karamar hukumar Shinkafi kuwa nan ma an hallaka yawaan bindiga da dama.

 

Sun kai hari yanlin ne bayan da su ka samu labari cewar Bello tunrji na shirin. Yin wani zama da yan tawagarsa.w

 

An kaiwa sansanin naa Bello Turji harin ne a ranar 5 ga watan Najaifu u da mu ke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: