Gwamnatin Jihar Borno ta amince da sauya sunan Jami’ar Jihar Borno zuwa Jami’ar Kashim Ibrahim don girmamawa ga tsohon gwamnan Arewa na farko.

 

Gwamnatin ta amince da sauya sunan Jami’ar ne bayan taron farko da majalisar zartarwa Jihar ta yi a wannan shekarar ta 2025, wanda gwamnan Jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya jagoranta a gidan gwamnatin Jihar a jiya Litinin.

 

Taron wanda aka shafe sa’o’i shida ana tattaunawa akan al’amuran da suka shafi ci gaban Jihar ta Borno.

 

Kwamishinan yada labarai da tsaron cikin gida Farfesa Usman Tar a lokacin da yake yiwa manema labarai karin bayani bayan kammala taron, ya ce Majalisar zartarwar ta duba takardu 42, sannan kuma ta yi duba akan ayyuka da kuma nasarorin da gwamnatin Jihar ta samu a shekarar 2024 da ta kare, tare kuma da tunkarar shekarar nan da ta kama ta 2025.

 

Kwamishinan ya kara da cewa sauya sunan jami’ar zai tabbata ne bayan cika dukkan doka, da kuma tuntubar hukumomin da suka dace a bangaren ilmi, ciki har da COREN, NUC, da kuma JAMB.

 

Tar ya kara da cewa Majalisar ta amince da sauya sunan Jami’ar Jihar ta Borno zuwa Jami’ar Kashim Ibrahim, kuma tunu aka fara aikin gyara akan dokar da ta kafa jami’ar.

 

Kazalika Kwamishinan ya ce majalisar ta kuma sake amincewa da sauya sunayen tituna, tare da sake lambobin gidaje a Maiduguri da sauran sassan Jihar don sabunta birane.

 

Tar ya bayyana cewa a halin yanzu garin Maiduguri na kara ci gaba sosai, sannan sabbin gine-gine da aka yi da tituna na bukatar a sanya musu sunaye domin ganin an inganta tsare-tsaren birane Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: