Akwai yiwuwar farashin man fetur ya sake hawa sama a Najeriya yayin da farashin gagar mai ya kai dala 80 a kasuwar duniya.

 

A makon da ya gabata farashin gangar mai na kan dala 73.

 

Tuni manyan ƴan kasuwa su ka ƙara farashin litar zuwa naira 950 kowacce lita.

 

Karin kaso 4.74 kenan aka samu a baya bayan nan

 

Manyan masu dorawa motocin dakon mai sun koma siyar da kowacce lita zuwa naira 950 sabanin naira 909 da ake siyarwa a baya

 

Yayin da wasu ke dorawa motocin dakon man a kan naira 960 kowacce lita

 

A baya an samu ragin kusan naira 100 kan kowacce lita ko da dai yan kasuwar ba su siyar da litar man kan naira 935 ba a mafi yawan gidajen mai kamar yadda su ka alkawarta.

 

Tun tuni dai kamfanin mai mai zaman kansa na NNPCL ya tsame hannunsa daga kari ko ragi na farashin litar mai yayin da kasuwa ke halinta bayan sakin man domin nemowa kansa da kansa daraja a kasuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: