Mutane takwas ne su ka rasa rayukansu sakamakon wani hatsarin mota da ya faru a jihar Neja.

Waɗanda su ka mutu ana kyauta zaton manoma ne.


Lamarin ya faru a titin Batati zuwa Lanle yayin da wata mota kirar Toyota da wata kirar Tirela su ka haɗu.
Waɗanda su ka mutu manoma ne da ke kokarin gudun hijira daga kauyen Dazu a karamar hukumar Lavun ta jihar saboda rashin tsaro.
Wani da lamarin ya faru a kan idonsa ya ce hatsarin ya dauki hankali matuka.
Aa cewasa ya kamata hukumar kiyaye afkuwar haddura ta ja kunne direbobi kan gudun wuce saa da su ke yi.
Mataimakin kwamandan ƙungiyar kula da matafiya ta Najeriya Kutigi Branch ya tabbatar da lamarin, wanda ya nuna cewar abu ne mai taɓa zuciya.
A cwarsa, ya kadu matuka daga abinda ya gani, wanda ya yi musu fatan dacewa.
Sannan ya yabawa hukumar kiyaye afkuwar haddura da hukumar ba da agaji ta Red Cross da sauran hukumomi bisa gudunmawar da su ka bayar.
Tuni aka binne gawarwakin a kauyen Dasu jiya Talata.