Hukumar sadarwa a Najeriya NCC ta amince da karin kaso 50 na kidin kira da data da aika sakon kar ta kwana.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Reunen Muoka ya fitar, sanarwar ta ce an sassauta karin da kaso amsin sabanin kaso 100 da kamfanonin layukan waya su ka bukata

Sannan karin na karkashin sashe na 108 na kudin dokokin hukumar sadarwa na shekarar 2013.

Tun a makon jiya ministan sadarwa ya tabbatar da cewar karin kudin kiran da zaa a yi zai kai kaso 30 zuwa 60.

Kamfanonin me su ka bukaci karin kudin, a cewarsu ba za su iya ci gaba da ayyuka ba har sai sun yi karin saboda sauye-sauye da aka samu a bangaren tattalin arziki.

Gwamnatin Najeriya ta ce ba da jimawa ba za a yi karin kuka ya fara aiki domin inganta hanyoyin sadarwa na ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: