Gwamnatin jihar Kano ta jinjinawa Matashiya TV, bisa ƙoƙarinta na ayyukan da su ka shafi ci gaban al’umma musamman na karkara.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan a wata ziyarar taya murna da shugabannin tashar su ka kai masa a yau Laraba a ofishin sa.

Kwamishinan ya kuma buƙaci sauran ƴan jaridu da su yi koyi da tashar, wajen ayyukan binciko matsalolin al’umma musamman mazauna yankunan karkara da sanar da gwamnati don magance su.

Inda ya kafa hujja da Ire-iren ayyukan da gidan talabijin na Matashiya TV ta ke yi na lalubo matsalolin al’umma da sanarwa da mahukunta, kama daga matsalar ruwan sha, asibitoci makarantu, hanyoyi da sauransu.

Ya kuma ƙara da cewa, tun da daɗewa ya san irin ayyukan da talabijin ta Matashiya TV ke yi na taimakon al’umma, ta hanyar kawo rahotanni da su ka shafi matsalolin al’umma kai tsaye, da ziyartar yankunan karkara don binciko irin ƙalubalen da su ke fuskanta dan sanar da mahukunta su ɗau matakin da ya dace.

Da yake jawabi tun da farko shugaba kuma babban editan Matashiya TV Alhaji Abubakar Murtala Ibrahim ya bayyana cewa, maƙasudun ziyarar ta su shi ne don taya murna ga kwamishinan, da kuma ƙulla alaƙa da ma’aikatar don ci gaban al’ummar jihar Kano.

Ya kuma ƙara da cewa, sun zaɓi yin irin wannan ziyarar ne a karon farko tun kafuwar tashar, duba ga yadda tsare-tsare da gwadaben tashar su ka yi daidai da ƙudurin kwamishinan na ci gaban al’umma, kama daga taimakawa mararsa ƙarfi da al’ummar yankunan karkara, ta hanyar zaƙulo matsalolinsu da magancewa.

Sannan ya jaddada cewar tashar za ta ci gaba da yin ayyukanta kamar yadda ta saba ba tare da gajiyawa ba.

Tawagar da su ka kai ziyarar, sun haɗar da manajan tashar Dakta Ashir T. Inuwa, shugabar ma’aikatan tashar Khadija Ahmad Tahir da waau ma’aikatan tashar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: